An tsare wani matashi a jihar Adamawa bisa zarginsa da daba wa mahaifiyarsa wuka a zazzafar takaddama da ta barke a tsakaninau. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ibrahim Umar mai shekaru 22 a karamar hukumar Michika da ke arewacin Adamawa an tsare shi a gidan yari bayan da ya amince ya daba wa mahaifiyarsa, Hajiya Lami Mallum wuka, a yayin wata takaddama da ta barke.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sako Fasinjoji Hudu Da Aka yi Garkuwa Da Su A Jihar Rivers
Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kamar yadda yake kunshe a cikin rahoton farko (FIR) da aka karanta masa a gaban kotu.
Babban Kotun Majistare da ke Yola, karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Buba, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma tare da dage sauraron karar zuwa wata mai zuwa, 18 ga Oktoba.
Takardun kotun sun nuna a ranar Talata cewa gardama, wadda ba a bayyana ba, ta shiga tsakanin wanda ake kara da mahaifiyarsa a makon jiya, 12 ga watan Satumba.
Rikicin ya rikide zuwa fada inda aka ce Umar ya daba wa Hajiya Lami wuka a fuska, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mahaifiyar wadda aka bayyana a matsayin sanadiyar mummunan rauni da yayi mata.
Matar da aka garzaya da ita babban asibitin Michika na ci gaba da karbar magani.
Mahaifiyar da ɗanta sun fito daga garin Zibadari dake karamar hukumar ta Michikaa jihar Adamawa.
A WANI LABARIN KUMA: Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Gidaje 400 A Jihar Filato
Biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe kwanaki ana yi, ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje kusan 400 a wasu sassan gundumar Pilgani da ke karamar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato.
DAILY POST ta ruwaito cewa yankunan da lamarin ya fi shafa sun hada da Zamadede, Shilur, Pishe, Angwan gani, Galang, da dai sauran sui.