Jama’ar shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun shawarci ‘ya’yan jam’iyyar PDP da su manta da batun takarar shugabancin kasa a zaben 2023, duba da irin yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo sauyi a kasar nan cikin kankanin lokaci. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Wannan jawabin ya fito ne daga bakin mai baiwa shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara ta kafafen watsa labarai, Garba Shehu, bayan kammala Sallar Idi a Abuja.
Kamar yadda ya fada, shugaban Kasa Muhammadu Buhari na samun goyan baya mara misaltuwa ba ga yan garin shi kadai ba, a baki daya kasar nan, wannan kadai ya isa ga jam’iyyar adawa data san cewa ba za ta iya komai ba a babban zabe mai zuwa.
KARANTA:- 2023: Garambawul ga Kundin tsarin zabe yunkuri ne na magudi, Cewar wasu jam’iyyu
Yace shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zama babban kalubale ga jam’iyyoyin adawa.
Garba Shehu ya cigaba da cewa, duk da mun san cewa jam’iyyar PDP da sauran na kokarin ganin sun kwace mulki a babban zabe mai zuwa.
Yace babu yadda za’ayi jama’a su bar shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma Jam’iyyar APC.
Garba Shehu ya Kara da cewa yan Najeriya suna jira ne kawai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna musu wanda zai gaje shi wajan gina kasa da habbaka tattalin arziqin kasar kawai.
Mai magana da yawun shugaban kasan yace, babu yadda za’ayi Yan Najeriya suyi gangancin dauko wata jam’iyyar don cigaba da mulki a zabe mai zuwa.
A wani labarin Iftila’in Kwalera: Mutane 30 sun mutu 2,000 na kwance a Asibiti a Jigawa
Tun barkewar cutar Kwalera a kasar nan kimanin Mutane 30 suka mutu inda sama da mutane dubu biyu ke kwance a Asibitoci daban-daban a Jihar Jigawa.
Dakta Salisu Mu’azu Sakatare na dindindin na hukumar lafiya na Jahar Jigawa ya tabbatar da wannan.
Yace kaso mafiya yawa wadanda ke dauke da cutar yara ne, a gaba daya kananan hukumomi tara da cutar tai kamari.
Dakta Salisu Mu’azu ya lissafo wadan su garuruwa da abin yayi kamari kamar su Hadejia, Dutse, Kirikasamma, Birnin Kudu da Ringim da saura wadan su wanda kutar ta leka.
Yace Kawo yanzu dai sama da mutane dubu biyu ne suke fama da cutar, wadansu suna kwance a Asibitocin gwamnati daban-daban wasu kuma sun gidajen su.
Sakataren bai dai ce ga musabbabin aukuwar lamarin ba, sai dai yafi dangata lalurar barkewar cutar Kwalera a Hadejia da rashi ruwa mai kyau.
Da yiwuwar akwai wani yanki da har yanzu suna bayangida a waje kuma ruwa na biyowa ta wajejen.
Dakta Salisu Mu’azu yace gwamnatin Jahar na iya bakin kokarin ta don ganin ta shawo kan matsalar.
Sakataren hukumar ta lafiya na Jigawa yace hukumar da take tallafawa kananan yara watau UNICEF, ta aiko da Magunguna da dama, ta kuma yi alkwarin sake aiko da wadansu da dama.