Yayin da ake tinkarar zaben gama gari na shekara ta 2023, wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a da jam’iyyun siyasa a kasar nan sun ce shirin kin amincewa da gudanar da zabe ta intanet da majalisar dokoki ke yi yunkuri ne na magudi.
Idan za a iya tunawa an mika bukatu da dama gaban majalisar kan garambawul ga kundin zabe na shekara ta 2010 don bada damar aiwatar da tsarin gudanar da zaɓe ta intanet.
Da suke zantawar bai-daya da Jaridar Peoples Daily, wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci yan kasa da su bijirewa wannan mataki na majalisar.
Lemar masu ruwa da tsakin ta kuma lura cewa wannan yunkuri da majalisar je yi na kin amincewa dokar, ya biyo bayan lura ne da ƴaƴan majalisar suka yi cewa ba lallai ba ne a sake zabarsu zuwa kujerarsu kamar yadda aka yi baya.
Idan za a iya tunawa a ranar Alhamis, majalisar dokokin ta ce muddin ana son aiwatar da zabe ta intanet to dole ne sai tsarin ya biyo ta karkashin hukumar kula da sadarwa ta kasa don tabbatar da tsaron kuri’un alumma.
Daya daga cikin yan jam’iyyun da ya yi tsokaci Shugaban Inter Party Advisory Committee Leornad Nzenwa ya ce abinda majalisar ke kokarin yi wata rufa-rufa ce kawai da ake kokarin kassara dimokuradiyar Najeriya.
Comments 1