Wani babban Malami a Jahar Kaduna, Sheik Ibrahim Asadus-Sunnah, ya shawarci Yan Najeriya da su dake wurin yima kasa addu’oi na zaman lafiya fiye da yawan korafe-korafe kan abun da ke aukuwa. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Asadus-Sunnah, shine Malamin da ya jagoranci Sallar Idi a Tudun Wada Bashama a Jahar Kaduna, yace mutane su dage da yima shuwagabannin addu’oi da sa ran abubuwa za su sauya nan gaba kadan.
Yace addu’oi ne kadai za su sanya shuwagabanni a kan hanya madaidaiciya, ta kuma ba su ikon aiwatar da hakkin da ke kansu.
KARANTA:- 2023: Garambawul ga Kundin tsarin zabe yunkuri ne na magudi, Cewar wasu jam’iyyu
Malam yace “Da yardar Allah sai kasar nan ta shawo kan matsalolin ta, da kuma rashin tsaro dake addabar kasar.”
Malam ya cigaba da cewa” Matuka mutane za su cigaba da addu’oi da izinin Allah matsalar kashe-kashe, satar mutane, yin fashi da makami zai zama tarihi a kasar nan.”
Malam ya roki jama’a wadanda suka samu damar yin layya da kada su manta da makotansu, wadanda basu samu damar yin haka ba, wannan zai kara musu kauna da zaman tare.
Malam yace, babbar Sallah na kara tuna mana muhimmanci yin layya, kaunar juna, sada zumunta da sauran ibadu daban-daban.
Yin hakan zai sanya Allah ya ji tausayin mu, ya kawo mana sauki kan musifar dake addabar kasar mu.
A wani labarin Buhari ya zabi Farfesa Ibrahim Wushishi a matsayin Rijistaran NECO
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Farfesa Ibrahim Danlami Wushishi a matsayin sabon Rijistaran hukumar jarrabawa ta NECO.
A wata wasika mai kwanan wata, sha shida ga watan July 2021, wanda Ministan Ilimi Adamu Adamu ya rattabawa hannu, ta kunshi amincewa da zabin Farfesa Ibrahim wanda zai fara aiki a 12 ga watan July 2021, har na tsawon shekaru biyar.
Farfesa Ibrahim Danlami Wushishi, Farfesa ne a fannin Ilimin kimiyya, an haifeshi a biyar ga watan April, na shekarar 1965, ya tashi a garin Wushishi Jahar Neja.
Farfesa Ibrahim Danlami Wushishi Malami ne a bangaren Ilimi a Jami’ar Usman Dan-fodio dake Sokoto, kamin a maidashi zuwa Jami’ar kimiyya da fasaha dake garin Minna Jahar Neja.
Har izuwa lokacin da aka bashi mukamin Rijistaran hukumar jarrabawa NECO, Farfesa Ibrahim Danlami Wushishi Malami ne a fannin kimiyya a Jami’ar kimiyya da fasaha dake Minna Jahar Neja.