Sabon Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa ya yi kira ga Iyaye da su yi amfani da wannan damar wajen kai ‘ya’yansu kanana wadanda shekarunsu bai wuce wata tara zuwa shekara biyar ba a duniya domin yi musu allurar kyanda.
Tsanyawa, ya yi wannan kiran ne a yayin da ya fara aiki a matsayin sabon Kwamishinan lafiya a jihar, a ranar Asabar, inda ya nemi goyon bayan ma’aikatan da ma al’umma wajen ganin ya gudanar da ayyukan da aka dora masa.
Sabon Kwamishinan ya karbi ayyukan yi ma’aikatar lafiyar ne daga hannun Sakataren ma’aikatar lafiyar, wato Alhaji Usman Muhammed, inda ya yi alkawarin ganin ya yiwa al’ummar jihar Kano iya bakin kokarinsa.