Hukumar zabe INEC ta bukaci shugabanin al’umma da sarakunan gargajiya su yi amfani da mukaman su wajen ganin an gudanar da zaben Gwamnan ranar 16 ga watan Nuwamba lami kafiya ba tare da wani mastala ba.
Shugaban hukumar a jihar Kogi, Dakta James Apam, ya mika wannan bukatar yau Jumm’a a yayin da yake jawabi a taron da hukumar ta yi da Sarakun gargajiya da shugabannin al’umma a jihar.
Apam ya kuma ce, ba zai taba yiwu wa ba a gudana da sahihin zabe in har ana tashin hankali, a saboda haka ya nemi shugabanin al’ummar dasu taimaka wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a fadin jihar a yayin gudanar da zaben da kuma lokacin da aka sanar da sakamakn zabe.
Ya kuma bukaci su kai rahoton duk wani da suke ganin zai iya yin barazana ga zaman lafiya a yankinsu a lokacin gudanar da zaben.
Kwamishinan ya kuma bukace su, da su taimaka wajen ilimantar da al’ummarsu yadda ake jefa kuri’a don hakan zai taimaka wajen rage irin kuri’un da ke samu sun lalace a yayin kirgar kuri’a.
Ya kuma kara tabbatar da kudurin hukumar na ganin an gudanar da sahihn zabe tare da yi wa dukkan yan takara adakci.
A nata jawabin, wakiliyar tarayyar Turai, Misis Maria-Teresa Maurio,ta yaba da yadda aka gudanar da taron, ta kuma ce, lallai ana bukatar kowa da kowa ya bayar da nasa gudumawar don samun nasarar zaben da za a gudanar.
Dakta Isiaka Yahaya, ne ya wakilci Misis Maria-Teresa Maurio a wajen taron ya kuma ce, sarakuna na da matukar mahimmanci a cikin al’umma don sune masu kai komo a tsakanin mahukunta da wadanda ake mulka.
Daraktan hukumar mai kula da ilimantar da masu zabe, Mista Ayo Aluko, ya ce, makasudin taron shi ne ilimantar da shugabanin al’umma kafin a gudanar da zaben.