Majinyata dake kwance a Asibitin koyarwa na Ahmadu Bello dake Shika a Zariya sun nemi gwamnati da ta tausaya ta yi sulhu da ma’aikata lafiyar da suka tafi yaji aiki na gargadi a kasar baki daya. Wakilinmu ya ziyarci asibitin don ganewa idonsa halin da ake ciki.
Asibitin koyarwa na Ahamadu Belle asibiti ne dake da matukar tarihi ta kowace fuska a kasa baki daya. A don haka duk lokaci da ka ziyarci asibitin sai ka riske wani abin karuwa da ya shafi kiwon lafiya kuma asibiti ne da take taka rawar gani a wajen kiwon lafiya. Wanda duk lokacin da aka sami matsala ta yajin aikin ma’aikatan lafiya na kowanne reshe, hakan na taba kasa ne baki daya.
Hakan ya sa wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban asibitin game da ko wani irin mataki hukumar Asibitin ta dauka ganin yadda marasa lafiya ke fadawa cikin mawuyacin hali?
Farfesa Ahmad Umdagas Hamidu shi ne shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda a jawabin da ya yi ya ce tuni suka dauki mataki kamar yadda aka saba. Shugaban ya ce da yake ba likitoci ne suke yajin aikin ba, a don haka akwai tsari da asibitin ke da shi na ko ta kwana kuma tuni tsarin ya fara aiki.
Shugaban ya ce amma duk da haka wajibi ne a bi duk hanyar da ta dace don magance matsalar, hakan ya sa hukumar lafiya ta kasa ta bayar da damar mu tura masu jadawalin kudin da ma’aikatan ke bi don daukar mataki kuma aikin na ci gaba.
Karshe shugaban ya kara da lasan takobi akan fitar da asibitin kunya ta bangarori da dama kamar yadda ya fadi.
Wakilinmu ya ziyarci dakunan majinyata dake harabar asibitin don ganewa idonsa halin da majiyatan ke ciki. Haruna majiyanci ne, a bayaninsa a yayin zantawarsa da wakilin namu cewa ya yi; “Gashi ina da karaya a kafata kuma ma’aikatan asibit duk sun tafi yajin aiki sai likitoci kuma likita ba zai yi shara ba kuma ba zai ciro kati ba, a don haka muna rokon gwamnati da ma’aikatan lafiya su yi wa Allah da Annabi su sulhunta domin talaka ne zai sha wahala masu kudi ba sa zuwa asibitin gwamnati, don haka a taimaka mana.”
Ya zuwa hada wannan rahoto, bincike ya tabbatar mana cewa a cikin kashi 100 na marasa lafiyar, kashi 99 sun kwashe kayansu sun bar asibitin masu hali kuma sun koma asibitin kudi don ci gaba da karbar magani.
Su kuma kungiyar ma’aikatan suna ci gaba da fafutukarsu na neman hakkokinsu da suke bi wanda ya yi sanadiyyar fadawarsu yajin aikin.