Yau Laraba 27 ga watan Almuharram/1442, wanda yayi dai-dai da 16 ga watan Satumba na shekarar 2020.
Ga cikakkuna labaran:
Tshohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewar lokacin daya miƙawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mulkin ƙasar nan lallai ƙasar bata lalace kamar yanzu ba.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da muƙarrabansa sun fitar da ƙaddamar da tambarin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai.
Shugaban Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta haramta shigo da kayan abinci ne don inganta noma.
Gwamnati tarayya ta rage kasafin kuɗin fadar Shugaban ƙasa daga naira biliyan 15b zuwa naira biliyan 10b a sabuwar shemara mai kamawa ta 2021.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewar ta kashe naira milyan 159 wajen gyara tsangayun almajirai na kwana a faɗin jihar.
Femi Fani Kayode ya ce matuƙar shugaba Buhari bai yi da gaske ba nan da shekarar 2023 babu wani abu da zai rage a Najeriya.
Wani gini mai hawa daya ya rufta tare da iyalai ‘yan gida daya a Kano, mutum biyu sun mutu.
Ingila ta yi barazanar sanya haramci kan duk wani ɗan Najeriya da aka samu da hannu a rikicin zaɓe.
Amurka ta ƙaƙabawa matar tsohon shugaban ƙasar Gambia takunkumi wato Jammeh.
‘Yan sanda sun kama sojoji kusan 100 kan zarginsu da alaka da mai wa’azin Musulinci a Turkiyya.
Tanzania ta ɗage haramci da ta kakaba wa kamfanonin jiragen saman Kenya.
Wasanni:
Akwai yiwwuwar Gareth Bale ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham wato tsohuwar ƙungiyar sa kenan.
Sergio Reguilon ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila.
Awasan sada zumunci da Barcelona ta fafata da Girona Philippe Coutinho da Messi sun jefa kwallo