Shugaban Kungiyar al’ummar Ijaw dake kudancin kasar nan Farfesa Benjamin Okaba ya tabbatar wa Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah cewa muddin ta tattara ta fice daga daular Najeriya kamar yadda ta yi ikirari, to lallai Ƙungiyar ta Ijaw za ta fi sakata ta wala.
Farfesa Benjamin Okaba yana maida martani ne dangane da ikirarin da Kungiyar Miyetti Allah ta yi ta bakin Sakataren ta Alhassan Saleh inda ya ce kungiyar ta shirya tsaf ta dare a kasar ta yi tata kasa.
Mista Okaba ya kara da cewa ko da yake ganawar da gwamnoni 17 na shiyar kudu suka bai zo a kan gaba ba, to amma Ƙungiyar Ijaw tana nan daram kan takardar bayan ta da gwamnonin suka fitar.
Ya kuma ce Al’umma Ijaw sun yi imani da ci gaba da dunkulewar kasarnan, to amma fa muddin babu gaskiya da adalci to ba ta tare da ita.