Fasto Samuel Kakande daga wata Cocin Uganda ya bukaci fara sabuwar shekara da dalleliyar mota, kuma ya ce mabiyansa ne za su siya masa, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon gabatarwarsa ta kai-tsaye, faston ya bayyana cewa motarsa da yanzu haka yake hawa kanta mabiya ne suka siya masa, amma ta tsufa kuma tana bukatar a sauyata.
KU KARANTA: Ku daina rugawa zuwa ga fastoci don yin addu’a, ku yita da kanku, Kumuyi ga kiristoci
“Ina bukatar Dala 300 daga kowa. Za a hada ne a siya min dalleliyar mota. Ina tukawa ina yi muku addu’a. Menene laifin hakan?”
Kamar yadda yace. Ya yanke wata ayar Luke, inda yace idan ka bayar za a biya ka.
Kakande ya bayyana cewa Dala 300 wato N130,000 akalla, wadanda ke da halin biyan fiye da hakan za su iya bayarwa daidai karfinsu.
Mabiya da dama sun yi alkawarin hada kudi su siya masa yayin da suke neman albarka a hannunsa.
Peter Obi Dan Kasuwa Ne, Bai Shirya Takarar Shugaban Kasa Ba –Fasto
Babban Faston Cocin Awaiting The Second Coming Of Christ Ministry dake Akure, Adewale Giwa, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi a matsayin dan kasuwa da bai shirya mulkin Najeriya ba.
Daily Post ta ruwaito cewa, Giwa, wanda yake jawabi ga mabiya cocinsa a Akure, jihar Ondo, a ranar Lahadi, ya ce farin jinin Obi a shafukan sada zumunta zai dusashe makonni kadan kafin zaben shugaban kasa na 2023.
A cewar malamin, ‘yan takara biyu ne kawai na jam’iyyar PDP da na jam’iyyar APC za su fafata a zabe mai zuwa.