Jam’iyyar Labour a Jihar Ogun ta kori Babban Daraktan majalisar yakin neman zaben Shugaban Kasa na Peter Obi, Doyin Okupe.
An kori Okupe ne tare da wasu mutum 10 bisa zarginsa da laifin rashin zama memba, shugaba da kuma rashin kudi.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Shugaban jam’iyyar a jihar Ogun, Michael Ashade, ya sanar da matakin da jam’iyyar ta dauka a Abeokuta ranar Alhamis, inda ya ce laifukan sun sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar Labour.
KU KARANTA KUMA Peter Obi Ya Bukaci Matasa Su Kwato Najeriya Daga Hannun Miyagu
Ashade ya ce Okupe ya daina zama memba na jam’iyyar saboda “rashin cika ka’idojin tsarin mulki na wajibi don cika matsayin membobinsa.”
A cewarsa, Okupe ya gaza biyan mambobinsa hakkokin zama mamba tun watanni shida da ya koma jam’iyyar, inda ya ce ya yi watsi da matsayinsa na jam’iyyar Labour, don haka bai cancanci zama babban Darakta na kwamitin yakin neman zaben Obi ba.
Ya bayyana cewa laifukan Okupe amd da sauran mutane guda 10 sun sabawa sashe na 9(3) sub(iii) da sashe na 9(3)xi na kundin tsarin mulkin LP.
Ya zargi Okupe da karkatar da kudaden da aka amince wa jam’iyyar ta LP a Ogun domin tara mambobin taron gangamin da aka gudanar a makon jiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa Yayin da suke sanar da shugaban jam’iyyar LP na kasa Barista Julius Abure shawarar da suka yanke, sun yi kira ga Obi da ya gaggauta nada wani babban daraktan PCC daga Arewa.
A Wani Labarin Kuma Tsagin G5: Dole Ne Babban Alkalin Alkalai CJN Yayi Murabus, In Ji Kungiyoyin Arewa
Dangane da tsokacinsa kan tsagin G5 na jam’iyyar PDP, Alkalin Alkalan kasar nan, Olukayode Ariwoola, na ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda wata gamayyar kungiyoyin arewa 52 suka ba da shawara a ranar Alhamis.
Kungiyar ta ce kasar ba za ta iya samun ingantacciyar dimokuradiyya ba tare da tsarin shari’a na gaskiya da adalci ba.