Wani Malamai mai suna Alhaji Kamaldeen Adeyemi-Bagudu, ya shawarci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen gudanar da addu’o’i da rokon Allah ya kawo karshen cutar Korona.
Shehin Malamin ya ce akwai bukatar Musulman kasarnan su dage da addu’a a daidai wannan lokacin wajen neman Allah ya kawo karshen annobar nan da ta addabi duniya.
Adeyemi-Bagudu, wanda shi ne Babban Limamin Masallacin Okitiipupa dake karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo, ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a garin Okitipupa. Inda ya kara da cewa wannan annobar ya fi karfin tunanin mutum, a nemi taimakon Allah kawai ne.
Shehin Malamin ya ce cutar ta yi illa matuka a bangaren tattalin arziki, siyasa, ilimi, addini da kuma harkokin kasuwanci ba kawai a Nijeriya ba harda ma sauran kasashen duniya baki daya, wanda hakan ya jefa al’umma cikin dimuwa.