Shugaban Hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Tukur Buratai ya nemi da a karawa bangare soji kudi domin magance matsalolin tsaron da ke ci gaba da addabar kasarnan tare da yaki da ta’addanci.
Ya yi wannan kiran ne a yayin bude wani taro karo na 12 kan horas da jami’an sojin wanda ya gudana a birnin Uyo a ranar Litinin. Buratai wanda GOC na runduna ta 6 ya wakilce shi wato Manjo Janar Jamil Sarham, ya ce kudaden da yanzu ake zubawa a bangaren soji idan aka yi duba da irin gudummawar da sojoji ke takawa wajen magance matsalolin tsaron cikin gida ya yi kadan.
Taken taron a wannan karon shi ne; “Fadada gudummawar sojojin Nijeriya wajen magance rashin tsaron cikin gida; bukatar gaggawar kudi.”
Ya ci gaba da cewa; sashen tsaron soji yana da bukatar a yi masa kwaskwarima kamar ta fuskancin hanyar rashin amfani da takardun kudi, da kuma tsarin amfani da asusun bai daya, da kuma tsarin IPPIS domin dakile fitar kudade ba bisa ka’ida ba.