Wata dirarriyar mai wasan barkwanci a kafafen sada zumuntar zamani, Ashmusy ta janyo wa kanta caccaka bayan bayyana kudin da take kashe kullum a hidindimun yau da kullum, instablog9ja ta ruwaito.
A cewarta, akalla ko wacce rana tana kashe Naira miliyan biyu akan kananun hidimomi. Kamar yadda ta nuna, hakan ya zamar mata jiki amma ba ta taba bayyanawa ba sai yau don sanin ko ita kadai ce hakan ke faruwa da.
Kamar yadda ta shaida a wallafar da tayi a shafinta ta fara ne da cewa:
“Don Allah ni kadai ce ke kashe akalla miliyan biyu a matsalolin yau da kullum? Ina nufin kullum. Ni kadai ce?
“Ban san ta inda ake samun hanyoyin kashe kudaden nan ba amma tabbas su na zuwa. Su na fadowa ne kamar manna daga sama. Biya N400,000 na wancan, biya N700,000 na wannan da sauransu. Amma ya haka. Ace kullum.”
KU KARANTA: Birtaniya ta biya diyyar kashe kananan yara 64 a Afghanistan
Gwammanatin Birtaniya ta biya diyyar mutuwar mutane da suka rasa rayukansu A Afghanistan wanda ya zarce yawan yaran da suka rasa rayukansu a ƙasar da kusan sau huɗu. Kamar yadda BBC ta ruwaito
Gwamnatin kasar ta bayar da diyyar ne ta mutuwar yara 64 , adadin da ya zarce mutum 16 ɗin da ta bayyana ta amince da su.
Dukkanin su sun rasa rayukansu ne sanadiyar yaƙin da sojojin Birtaniya suka fafata daga shekarar 2006 zuwa 2014.
Sabbin alƙalumman sun fito ne daga bayanan kare haƙƙin bil’adama da ƙungiyar bayar da agaji a ɓangaren tashe tashen hankali da ya shafi sojoji wato action on Armed Violence (AOAV) ta nema.