By Abbas Yakubu Yaura
Wani dalibi mai matakin ajin 4 a Sashen Falsafa na Jami’ar Jihar Ekiti dake Ado-Ekiti, Ayodeji Aderobaki, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Yaba, Jihar Legas, bisa zarginsa da damfarar wani Tobbena Okolo, naira miliyan 4.7m.
Ana zargin Aderobaki da lafin damfarar Okolo kudaden a watan Agustan shekarar 2021.
An gurfanar da matashin mai shekaru 22 a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi hada baki, karya da kuma sata.
Sai dai ya musanta zargin da ake masa.
A wani bangare na tuhume-tuhumen ya kara da cewa, “Kai, Aderobaki Ayodeji, da sauran su, a wani lokaci a cikin watan Agustan shekarar 2021 a kan titin Adeyinka Okunade, cikin garin FESTAC, a karamar hukumar Amuwo Odofin, jihar Legas, a cikin gundumar Legas, kun yi makarkashiya tare da aikata manyan laifuffuka, dan samun kudi ta hanyar karya da sata, ta yadda za a aikata laifin da zai hukunta ka a karkashin sashe na 411 na dokar laifuka ta jihar Legas ta Najeriya shekarar 2015.
“Cewa, kai Aderobaki Ayodeji, da sauran jama’a, a rana daya, lokaci da wuri a gundumar Majistare da aka ambata a baya, kun sace dukiyar wani Tobbena Newton Okolo har Naira miliyan 4,700,000, wanda hakan ya sa kuka aikata laifin da za a yanke hukunci a karkashin sashe na 287. na dokar laifuka ta jihar Legas ta Najeriya 2015.”
Ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, yayin da alkalin kotun ya amince da bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 2m tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
An dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 9 ga watan Maris, 2022.