Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta ce dole ne yan majalisun yankin arewa su motsa yayin da ake gabda sanya hannu kan dokar sauya fasalin kasar nan.
Shugaban kungiyar Cif Audu Ogbeh shine ya mika takardar yayin da wasu jiga-jigan gwamnati suka ga dacen wannan mataki tare da bukatar kudirin kafa Masana’antar man fetur.
Waɗannan jiga-jigan mutane dai sun gudanar da sharhi da dama yayin wani taron da majalisar wakilai ta gudanar da aka mishi take da “Kudirin Kafa Masana’antar man fetur da kuma Alkiblar Najeriya”
Da yake magana a yayin taron, Audu Ogbeh ya ce Najeriya ta zama karan baya a kowane fage da ya shafi masana’antu da samar da ayyukan yi wanda kuma rashin taka rawa da manyan arewa ke yi shi ya gurgunta lamarin.