Gwamnatin tarayya ta gayyaci Likitoci dake shirin tsunduma yajin aiki da su zo su zauna a fahimci juna kan yunkurin na shiga yajin aikin a ranar 1 ga watan Afirelu mai kamawa.
Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige shine ya fadi hakan ta bakin Kakakin Ma’aikatar Charles Akpan inda ya ce wannan zama zai gudana ne a yau Laraba da misalin karfe uku na yammaci a Shelkwatar Ma’aikatar dake birnin tarayya Abuja.
Ana sa ran Shugaban Kungiyar shi zai jagorance ta yayin da shi kuwa Minista Ngige shi za jagoranci Ma’aikatar Kwadago da Ayyukan.
Idan za a iya tunawa dai fadar shugaban Kasa ta ce sai da ta gana da Kungiyar Ma’aikatan Jinyar gabannin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi balaguro zuwa birnin Landan don duba lafiyar shi.
Wannan yajin aiki na ma’aikatan jinya na zuwa ne Yayin da ake tsaka da fargabar barkewar annobar Covid-19 zagaye na biyu ne dai Ƙungiyar ma’aikatan jinyar ta ce muddin gwamnatin tarayya ba ta biya mata bukatun ta ba.