By Abbas Yakubu Yaura
Majalisar gudanarwa ta Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Offa, ta amince da nadin Dokta Olarongbe Afolabi a matsayin shugaban riko na makarantar daga gobe Laraba, 12 ga watan Janairu, 2022.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Olayinka Iroye, shugaban hukumar na cibiyar ta bayyana nadin Afolabi ta wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga watan Janairu, 2022 kafin nada sabon shugaban kwalejin fasahar.
Iroye ya bayyana cewa nadin mukaddashin shugaban cibiyar ya biyo bayan cikar wa’adin shugaban Kwalejin Dakta Lateef Olatunji ne a ranar 11 ga watan Janairun 2022.
An nada Olatunji a matsayin shugaban makarantar na 4 a ranar 12 ga Janairun shekarar 2017 wanda ya kwashe tsawon shekaru biyar yana aiki.
Sabon Shugaban riko ya kasance ma’aikaci na farko na a Kwalejin Fasahar bayan ya shiga makarantar a farkon shekarar 1992.
Har zuwa sabon nadin nasa, Afolabi ya kasance mataimakin shugaban hukumar (Gudanarwa) na cibiyar.