By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa reshen jihar Legas ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki uku.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa majalisar zartarwar kungiyar ta jiha a taronta na ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2021 ta kuduri aniyar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga ranar 10 ga watan Janairu zuwa 12 ga watan Janairun 2022.
Ma’aikatan jinya sun sanar da zasu fara yajin aikin ne a ranar Litinin din data gabata domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyan albashi da kuma yanayin aiki a bangaren kiwon lafiya na jihar.
Sai dai shugaban kungiyar ta NANNM na jihar, Olurotimi Awojide, bayan gudanar da taron gaggawa na kungiyar ya ce za a dakatar da yajin aikin ne domin baiwa gwamnati damar cika alkawuran da ta dauka.
Sannan ya ce, “Muna godiya ga gwamnan da ya mayar da martani cikin gaggawa; mun yi taron gudun hijira da shi da sauran masu ruwa da tsaki.Muna fatan za a fara aiwatar da bukatunmu nan take.
“A kan haka ne muka dakatar da yajin aikin don ba da damar aiwatar da bukatunmu. Ana sa ran duk ma’aikatan jinya a jihar za su dawo bakin aikinsu da karfe 8 na safiyar ranar Talata.”