Mahukunta Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi dake birnin Lokoja su Kori akalla Dalibai 194 a Makarantar sakamakon rashin kwazo a jarabawar Zangon karatun shekara ta 2019/2020.
Shugaban sashin hulda da jama’a da tsare-tsare ta makarantar Uredo Omale ne ta bayyana hakan a yau Alhamis a garin Lokoja.
Omale ta bayyana cewa, daliban da lamarin ya shafa sun hada da na sashin koyan harkar kasuwancin, Lissafin da kidugguga, kiwon lafiya daku sashin ilimin yada labaran.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalara ta kashe mutane 8, 66 sun kamu a jihar Kogi
Ta kara da cewa, hukumomin makarantar sun dauki wannan matakin ne na korar daliban, sakamakon yin nazarin kan sakamakon daliban a wani zama na gaggawa da suka gudanar
Kazalika ta ce, Mataimakin Shugaban makarantar Dakta Kehinde Felix Lamidi, Wanda shine ya jagoranci zaman gaggawan, ya amince da sakamakon jarabawar ta biyu, na zangon karatun shekarar 2019/2020 da sauran sakamakon da ake jira.
Omale ta kuma ce, Shugaban makarantan ya yaba wa kwamitin dake kula da sakamakon jarabawar makarantan, da kuma sauran mambobin kwamitin zartarwa na Kwalejin.
Ta kuma ce, Dalibai 9 an koresu ne a ajin farko ND1 na sashin Lissafin da kidudduga, 1 daga sashin kiwon lafiya, 130 Kuma daga sashin Koyan harkar kasuwancin, Dalibai 31 daga aji daya na Babban Diploma a sashin Koyan harkan kasuwanci, da dai sauransu.
Comments 1