Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Sojojin Saman Najeriya Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya yabawa rundunar sojin saman Najeriya bisa yadda ta tura jiragen Super Tucanos yadda ya kamata da kuma nasarar da aka samu ya zuwa yanzu kan kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.
Na’Allah ya yi wannan yabon ne a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Lahadin nan domin tantance ingancin ayyukan da hukumomin tsaro ke yi na sabbin jiragen yaki na Super Tucano.
Ya bukaci rundunar sojojin saman Najeriya da su ci gaba da gudanar da aiki mai kyau domin samun karin karfin gwiwa a kokarinsu na kawar da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/new-zealand-ta-buɗe-iyakokinta-tun-bayan-barkewar-cutar-corona/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Shugaban ya bayyana shawarar samun hanyoyi a matsayin daya daga cikin mafi hikimar da Gwamnatin Tarayya ta dauka ta fuskar tanadi da sassaucin aiki.
Ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da kara adadin domin rage tsadar tafiyar da Sojojin Sama.
(NAN)