Biyo bayan barazanar da wasu kungiyoyin ta’addaci suka yi na kaiwa wasu manyan biranen Najeriya hare-hare a jiya, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta tsaurara matakan tsaro a kusa da wuraren da ake gudanar da ibada da wuraren shakatawa a fadin jihar.
Dangane da barazanar harin ta’addancin da aka shirya kaiwa manyan biranen kasar nan da suka hada da Legas da Kuma babban birnin tarayya Abuja Wanda ya karade shafukan sada zumunta na zamani.
Idan za a iya tunawa, a cikin makon da ya gabata, ‘yan ta’adda sun kai hare-hare da dama a wasu unguwannin dake cikin birnin tarayya Abuja, inda suka yi ta kashewa tare da yin awon gaba da wasu da dama a lokacin faruwar farmakin.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Legas, Abiodun Alabi, ya ce an sanya hukumar leken asiri ta jihar (SIB) da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Harin Plateau: Wasu DA Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Yi Ajalin Mutum 8, An Jikkata 2 A Jos
Alabi, ya Kara da cewa rundunar na aiki tare da sauran jami’an tsaro domin samar da tsaro a fadin jihar, tare da ba mazaunan Legas tabbacin yin sana’arsu ta yau da kullun ba tare da wata fargaba ba.
A karshe ya umurci mazauna jihar Legas da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi akan duk wasu mutane da suke zargi ga hukumomin tsaro ba tare da bata lokaci ba.
A wani labarin kuma na daban
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Sojojin Saman Najeriya Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya yabawa rundunar sojin saman Najeriya bisa yadda ta tura jiragen Super Tucanos yadda ya kamata da kuma nasarar da aka samu ya zuwa yanzu kan kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.
Na’Allah ya yi wannan yabon ne a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Lahadin nan domin tantance ingancin ayyukan da hukumomin tsaro ke yi na sabbin jiragen yaki na Super Tucano.
Ya bukaci rundunar sojojin saman Najeriya da su ci gaba da gudanar da aiki mai kyau domin samun karin karfin gwiwa a kokarinsu na kawar da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.
Shugaban ya bayyana shawarar samun hanyoyi a matsayin daya daga cikin mafi hikimar da Gwamnatin Tarayya ta dauka ta fuskar tanadi da sassaucin aiki.
Ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da kara adadin domin rage tsadar tafiyar da Sojojin Sama.
(NAN)