Kwastam Sun kama kayayyakin da Darajar su takai Naira Miliyan 38.5 a Katsina
Kwanturola na Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa a Katsina Dalhatu Chidi-Wada, a ranar Alhamis yace yanayin yadda ake shigowa da kayayyaki ta ɓarauniyar hanyoyi zuwa Jahar, yanzu ya rage matuƙa gaya daga watan mayu na Shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu ɗauki tsatstsauran Mataki ga wanda suke bayan Matsalar Tsaron Najeriya — Buhari
Ya alaƙanta wannan cigaba da sake buɗe iyakar Jibia, wanda yace ya sanya mutane da dama suna kasuwancin su ta hanyar daya dace a yankin.
Wada, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga taron Manema Labaru akan aikace-aikacen Hukumar Kwastam a Katsina a watan Mayu na Shekarar 2022.
Shugaban Hukumar yace Rundunar ta samu nasarar kama kayayyakin da kuɗin su yakai Naira miliyan 38,575,887.00 a cikin watan da aka ambata na Mayu.
Wada ya kuma ƙara dacewa, yanayin kayayyakin da ake fita dasu ta hanyar iyakar Jibia a wannan lokaci, ya ƙunshi Ton na Man Gas da yawanshi yakai dubu 4,000, a yayin da Ton na Siminti aka fitar da wanda yakai 1,000.
Ya ƙara dacewa, buɗe iyakar Jibia ya bada damar gudanar da kasuwanci ta hanyar shiga da kayayyaki, da fitowa dasu yanda ya kamata, bata ɓarauniyar hanyoyi ba.
Shugaban Hukumar yace tuni sun ƙara matsa ƙaimi wajen magance fasa ƙwauri, da shigowa da kaya ba bisa ƙa’ida ba, ta hanyar kai samame, da samun bayanan sirri, da sauran su.
Comments 1