Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS), shiyyar jihohin Oyo da Osun a ranar Talata, ta kama wasu masu fasa kwauri 19 tare da kama wasu kayayyaki a kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Kayayyakin da aka kama sun hada da busasshen kifi, gumammiyar shinkafa, man fetur da kuma tanka.
Sauran sun hada da kunshin kayan sawa da takalma, motoci 17, tayoyin da aka yi amfani da su, buhunan tabar wiwi da kwalayen maganin kwari.
Da yake gabatar da kayayyakin da aka kama a hedikwatar hukumar a jiya laraba, Kwanturola, Mista Adamu Abdulkadir, ya ce rundunar ta tara sama da Naira Billiyan 80 ga gwamnatin tarayya tsakanin watan Nuwamban Shekarar 2021 zuwa watan Janairu, shekarar 2022.
Ya ce, “A tsawon lokacin, rundunar ta kama haramtattun Kayayyaki 356, tsare 46 da kuma kwace 19.”