Wani matashi mai suna Solomon Hangega daga Jihar Binuwai ya wallafa bayani akan yadda yake bukatar matarsa ta sunna ta kasance, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da wata Grace Fedelis ta tambaye shi idan shi ma namijin da ya dace a aura ne, matashin wanda ya kammala jami’ar Joseph Sarwuan Tarka, ya ce shi ma yana son hadaddiyar mace saboda iliminsa da kuma dukiyarsa.
Ya ce saboda yanayin kyawunsa, yanayin kamalarsa, iliminsa, aikinsa, yadda yake samun kudi kamar noma da kasuwanci tare da sauran abubuwa, yana tunanin ya dace ya auri haddiyar mace.
Ya ce duk macen da ke son aurensa to wajibi ne ta kasance daga karamar hukumar Logo ko ukum ko Gboko ko Kwande.
Akalla sai ta kammala ND a bangaren lafiya ko BA/BSC a wani bangaren ilimi banda shari’a ko jarida.
Wajibi ne ta kasance ta mai mazaunai madaidaita, kyakkyawar fuska, kumbuna masu kyau, idanu masu haske, fararen hakora, matsakaitan albarkatun kirji, ciki madaidaici, kafafu da hannayen da su ka dace.
Sauran sun hada da ayyukan dare, ta kasance mai ladabi, mai dagewa, mara samari, ta iya girki da sauransu.
Wajibi ne mahaifinta ya zama dan siyasa kuma mai arziki yayin da mahaifiyarta ya kamata ta zama mai aikin jinya ko malamar makarantar jami’a.
KU KARANTA: Ta kasance fara, budurwar da bata taɓa soyayya va kuma ta iya Larabci, Ɗan Najeriya na neman mata
Wani dan Najeriya ya bayyana abubuwan da yake bukata dangane da macen da ya ke so ya aura inda ya bayyana cewa wajibi ne ta kasance tana da duk abubuwan da ya lissafo, Legit.ng ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne ta kafar Twitter inda yace wajibi ne macen da yake son aure ta kasance ta iya larabci sosai kuma ta zama tana don ta koma duk inda ya yanke shawarar zai tafi da ita idan sun yi aure.
Banjo Hanjo, a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamban 2022 ya yi wallafar a Twitter inda yace dan uwansa ne ke neman matar aure. Ya ce da farko dai ta iya larabci sosai, idan har tana so a tantanceta.
Wajibi ne ta amince da bin da duk inda yaso su zauna. Kuma ta zama wacce ta iya soyayya ta yadda za ta siye zuciyarsa da zarar ya ganta.
Comments 1