Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Suleiman, a kan wani rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara a masarautarsa.
Mummunan tashin hankalin, wanda ya haddasa jikkatar mutane da dama, ya ɓarke ne a garin Hardawa na ƙaramar hukumar Misau kwana biyar da suka gabata.
Ɓangarorin biyu sun yi fito-na-fito ne a kan mallakar wani dajin gwamnati inda makiyaya suka daɗe suna kiwo, amma ƙaramar hukumar Misau ta yi ƙoƙarin mayar da shi gonaki, lamarin da ya fusata makiyayan, ya kuma kai ga rikicin.
Hakimin Chiromah da Dagacin Zadawa na cikin ayarin masu sarautar da aka dakatar.
Saboda wannan rikicin ne dai Gwamna Bala Mohammed ya dakatar da shugaban riko na ƙaramar hukumar ta Misau, Yaro Gwaram, a ranar Larabar da ta gabata.
A daidai lokacin ne kuma ya dakatar da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Baidu Kafin-Misau, da sakatarenta, Sarki Usman Abdu.