Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas, LASEMA ta taya matar da ta haihuwa a sansanin gudun hijira murna.
Matar mai suna Madubike Promise tana cikin wadanda gobarar Ebute-Egba ta shafa, inda take zaune a sansanin hijira na Igando.
Babbar Daraktan LASEMA din, Dr Olufemi Oke-Osanyintolu, ya shaidawa majiyarmu cewa Madubike ta haifi yaro a babban asibitin Alimosho da misalin karfe 6:40 na safiyar ranar Asabar.
A cewarsa, iyayen yaron sune Reuben da Promise Madubike, inda sansanin suka cika da murna bisa haihuwar yaron.