Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City dake kasar Birtaniya ta yi wuff da dan wasan gefe na Southampton Ryan Bertrand daga Southampton a matsayin kyauta.
Yanzu haka Bertrand zai lashe kaka biyu ne a Leicester City wato daga yanzu har zuwa 2023.
Dan wasan mai shekara 31 ya hade da Foxes ne bayan shafe shekara bakwai yana murza leda a Southampton yayin da ya fafata mata wasanni 240.
Idan ba a manta ba Leicester City ta karkare kakar Firimiyar bana ne a mataki na biyar bayan da ta ɓarar da damarta ta karshe ta zuwa gasar zakarun turai a wasan karshe.
Kazalika Bertrand ya taimakawa Chelsea lashe gasar zakarun turai ta Champions League a shekara ta 2012.