Ma’aikatan filin jirgin sama sun kawo cikas a harkokin zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Mallam Aminu Kano (MAKIA) sakamakon takaddamar da ta kunno kai tsakanin hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya NAMA.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa jiragen da zasu tashi daga Kano a safiyar yau litinin sun samu cikas yayin da jami’an kula da zirga-zirgar jiragen suka dakatar da ayyukansu wanda ya shafi sauka da tashin jirage.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An hana jiragen sama irin su AZMAN da Max Air da aka shirya zasu tafi Abuja da Legas su tashi.
karanta kuma: Ma’aikatan Kamfanonin Jiragen Sama Sun Sanar Da Dakatar Da Aiki
Daga baya an ce fasinjojin da suka shiga jirgin su sauka yayin da jami’an kula da zirga-zirgar jiragen suka rufe ayyukansu.
Solacebase ta sanar cewa kungiyar masu kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NATCA ta rufe ayyukan zirga-zirgar jiragen sama a ciki da wajen filin jirgin MAKIA kan samar da wutar lantarki ga cibiyoyin NAMA da ma’aikatan da abun ya shafa.
Wata majiya a filin jirgin ta shaida wa Solacebase cewa wasu muhimman mutane da suka makale a filin jirgin da suka hada da wasu ‘yan majalisar tarayya, mataimakan gwamnoni da sauran su tuni suka shiga tsakani domin warware sabanin da ke tsakaninsu ta yadda za a maido da aikin jiragen.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Jihar Kogi Ta Yi Jana’izar Gawarwaki Sama Da 100
Gwamnatin Kogi ta gudanar da jana’izar gawarwaki 130 da ba a bayyana masu su ba da aka ajiye a dakin ajiye gawarwaki na gwamnatin tarayya (FMC) da ke Lokoja.
Mrs Elizabeth Arokoyo, Babban Manajan Hukumar Kula da tsaftar muhalli da shara ta jihar Kogi ta bayyana haka yayin da take tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadin nan.