Gwamnatin Kogi ta gudanar da jana’izar gawarwaki 130 da ba a bayyana masu su ba da aka ajiye a dakin ajiye gawarwaki na gwamnatin tarayya (FMC) da ke Lokoja.
Mrs Elizabeth Arokoyo, Babban Manajan Hukumar Kula da tsaftar muhalli da shara ta jihar Kogi ta bayyana haka yayin da take tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadin nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Arokoyo wadda ta samu wakilcin mukaddashin sakataren hukumar Mista Ajayi Olufemi, ya ce an yi jana’izar gawarwakin ne a makabartar Felele a ranar Asabar.
Katanta kuma: Gwamnatin Kogi Ta Hana Hakar Ma’adanai
Ta ce gawarwakin da ba a kai ga samun mamallaka gawarwakin wadanda hatsarin ya rutsa da su ba, ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne da aka ajiye a dakin ajiyar gawa na FMC na tsawon watanni ba tare da iyalai ko masu alaka da su sun fito sun yi ikirarin nasu ba ne.
A cewarta, doka ta ba wa hukumar damar binne gawarwakin da ba a kai ga gano masu su ba a wani yunkuri na tabbatar da cewa muhallin ya kasance tsaftatacce.
Ta ce gawarwakin da jami’an ‘yan sanda da na hukumar kiyaye hadura ta tarayya suka ajiye a dakin ajiyar gawarwaki suna da yawa a dalilin haka aka yanke shawarar binne su.
“Mun bayar da sanarwa ta kafafen yada labarai da jaridu cewa masu alaka da gawawwakin su zo su yi ikirarin nasu ne amma kokarin bai samar da sakamakon da ake so ba,” inji ta.
Babban Manajan ta nanata kudurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa muhalli ya kasance a tsaftace ga mutane.
“Dukkan mutanen da ke kwashewa da binne wadannan gawarwakin an tsabtace su.
“Kamar yadda na fada a baya, mun yi sanarwa da dama a gidajen rediyo da talabijin da sauran kafafen yada labarai game da gawarwakin da ba a kai ga gano masu gawarwakin ba.
“Amma, yayin da nake magana da ku, ba a jin komai daga ’yan uwa, dangi, da abokan wadannan Gawarwaki ba.
“Don haka dole ne a binne su saboda sun dade a dakin ajiyar gawa ba tare da wani ya zo musu ba,” in ji ta. (NAN)
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Jihohi Su Mayar Da Dokad Kare Hakkin Nakasassu
Babban Sakataren Ma’aikatar Agaji, Cigaban Jama’a da Kula da Bala’oi, Nasir Sani Gwarzo, ya bukaci gwamnatocin Jihohi da su tabbatar da dokar hana wa nakasa wariya ta shekarar 2018 domin isar da ingantacciyar hidima ga duk masu nakasa a kasar nan.
Ya yi wannan kiran ne a Abuja a wajen bude taron shugabannin da ke da alhakin farfado da nakasassu a Najeriya.