Madugun ƴan adawan ƙasar Senegal Ousmane Sonko ya kawo karsehm yajin cin abinci da yake yi bayan cafke shi da hukumomi suka yi a watan Yulin bana.
Ana tuhumar Mista Sonko wanda na ɗaya daga cikin yan adawar shugaban kasa Macky Sall da zargin kawo husuma a ƙasar.
KARANTA WANNAN LABATIN: Sojojin Faransa: Dubban Mutane Sun Sake Gudanar Da Zanga-zanga A Nijar
Tuni dai aka haramta masa tsayawa takara a zaɓen baɗi bayan da aka sameshi da hannu dumu dumu da baiwa wata mata toshiyar baki.
Malaman addinin musulunci ne a ƙasar suka horeshi da kawo karshen yajin cin abinci da yake kasantuwar haramcinsa a addinin musulunci.
A watan jiya ne aka aika da Sonko sashen kula na gaggawa a wani babban asibitin dake ƙasar bayan da aka lura cewa ƙoshin lafiyarsa ya taɓarɓare.