Gwamnatin tarayya ta ce babu alamun tsimin da aka karbo daga kasar Madagascar zai warkar da cutar korona kamar yadda kasar take ikirari.
Ministan lafiya na Nijeriya, Osagie Ehanire shi ne ya sanar da hakan, inda ya tabbatar da cewa; cibiyar binciken magunguna ta kasar ta bayyana a cikin rahoton bincikenta cewa, maganin na Madagascar na da sinadaran da za su iya rage yawan tari ne amma ba waraka ce ga cutar korona.
A watan Afrilu ne shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya kaddamar da wannan tsimi, da ya yi ikirarin yana warkar da cutar korona.