A ranar Larabar da ta gabata ne mambobin jam’iyyar APC reshen jihar Osun da ke goyon bayan ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, suka yi taruwar farin dangoa hedikwatar ‘yan sandan jihar Osun da ke Osogbo, inda suka yi zanga-zangar nuna kyama ga Kwamishinan Yan sandan jihar.
Masu zanga-zangar karkashin jagorancin Rasaq Salinsile, shugaban kungiyar Aregbesola, na dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban.
Sun zargi kwamishinan ‘yan sanda, Wale Olokode, da goyon bayan gwamnan, Adegboyeg Oyetola.
Sun kuma bukaci a maye gurbin Kwamishinan Yan sanda da wani.
A wani labarin Kuma na daban.
Shari’ar Kanu: DSS sun ƙi kulle hanyoyi zuwa Kotu da Farfajiyar ta, sakamakon umarnin Kotu
Sashen Jami’an Tsaro na Farin Kaya a ranar Laraba, yabi shawarar da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a Abuja, na ƙin rufe Dukkanin farfajiyar Kotun da Kewayen ta, gabanin shari’ar Shugaban Ƙungiyar Tsagerun Biafra Nnamdi Kanu.
Mai Shari’ar Binta Nyako wadda ta sanya ranar yau, ƙarfe 1 na rana, ta shawarci Jami’an Tsaron na DSS dasu sanar da ofisoshin su akan shawarwarin data bayar.
Duk da dai Nyako bata bayar da umarni ba tana umartar Jami’an tsaro akan lamarin, tace bazata bari harkokin Kotun a tsaida su ba.
A dubawar da akayi da sanyin safiyar yau, ya nuna cewa, Ma’aikatan Babbar Kotu, da Lauyoyi, da Ƴan Jarida, da sauran su, an basu damar zuwa har inda ake gudanar da shari’ar da kewayen ta.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, akwai walwala na zuwa ko’ina, da ababen hawa ciki da wajen Kotun.
Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito cewar Joji a ranar 19 ga watan Fabrairu ta shawarci Jami’an tsaro na Farin Kaya da kada su mamaye wurin da sabon tsarin su na tsaro a Kotun, har sai zuwa ƙarfe 12 na rana.
Kotun ta bada umarni ga DSS dasu mamaye Kotun ne idan aka fara Shari’ar Kanu akan ta’addanci.
Nyako ta yi ƙorafi cewar shari’ar wasu yana shafar su duk lokacin da akace anyi shari’ar Kanu, sakamakon yawaitar jami’an tsaro da rufe hanyoyin zuwa Kotun.
Daga nan sai ta sauraron shari’ar ta’addanci ta Kanu zuwa Ƙarfe 1 domin ganin an kammala wasu shari’ar.
Comments 1