An kashe wani mai gadi mai suna Sunday a gidan man Titolu Venture da ke Igoba a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo.
Mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Litinin.
Maharan da suka kai masa hari sun far wa gidan man kafin su tsere. An ce an daure mai gadin gidan man kafin a harbe shi.
Manajan gidan Man Ajisafe Oluwatobiloba, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin da misalin karfe 4 na safe.
A cewarsa, “da misalin karfe 4 na safe, daya daga cikin mazauna garin ya kira ni, da isarsa, sai muka ga tmgidan man na tana ci da wuta; mun kira hukumar kashe gobara suka zo kashe gobarar, ba tare da sanin wadanda suka aikata laifin ba, kuma sun kashe jami’in tsaron mu.
“A yayin da ake kokarin gano abin da ka iya haddasa gobarar, mun ga inda aka daure mai gadin aka kashe shi. Haka kuma mun ga kwalbar da aka akayi amfani da ita cike da man fetur wanda wannan wani bangare ne da akayi amfani da shi wajen jika gidan Man kafin a cinna masa wuta.”
A halin da ake ciki, jami’an tsaro na ‘yan sandan Ondo da suka ziyarci wurin da lamarin ya faru sun ajiye gawar mai gadin a dakin ajiyar gawa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mrs Funmi Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu a faruwar wannan lamari.
A wani labarin kuma
A hukumance an ayyana bullar cutar Ebola ta baya-bayan nan a Kongo, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a ranar Litinin din nan.
Hukumad ta ce barkewar cutar ta shafi lardin Equateur da ke arewa maso yammacin kasar, inda aka samu bullar cutar ta farko a ranar 23 ga Afrilu.
Ya ce a cikin dukka, an tabbatar da kamuwa da cutar mutane guda hudu da kuma mutum daya da ake zargi da kamuwa da cutar, amma majinyatan duk sun mutu ne sanadiyyar cutar.
A wata barkewar da ta gabata a lardin tsakanin Yuni zuwa Nuwamba 2020, an gano jimillar mutane 130 kuma mutane 55 sun mutu.
Koyaya, barkewar sabuwar cutar ita ce ta 14 da aka rawaito a cikin ƙasar mai mutane miliyan 90 tun 1976.
A tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, cutar ta barke a mafi girman garuruwa a yammacin Afirka inda sama da mutane 11,000 suka mutu.
Cutar Ebola takan haifar da zazzabi mai zafi da zubar jini a cikin jikk, kuma tana yin barazana ga rayuwa. (dpa/NAN)