Akalla mutane hudu ne rahotanni suka ce an kashe a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al’umma biyu a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mazauna kauyen sun shaida wa jaridar Daily trust ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne tsakanin yammacin Juma’a zuwa safiyar Asabar.
“An kashe mata biyu a bayan makarantar firamare ta Yogbo da wata guda kuma a cikin al’umma a jiya Juma’a. Abin bakin ciki shine kauyen da shugaban karamar hukumar ya fito.
“A yau (Asabar) maharan sun kashe mutum daya a Ukohol. Sun kuma kona gidaje da dama a kauyuka da dama da aka kai hari a yankin,” in ji wani dan kauyen.
Karanta kuma: Gwamnatin Benue Ta kawar Da fargabar Barkewar Wata Cutar a Jihar
Wasu mazauna kauyukan kuma sun ba da labarin cewa mazauna garin sun kaurace wa wuraren da abin ya shafa saboda fargabar sake kai hari.
Shugaban Guma Mike Ubah, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin a wani sako da ya aiko.
Ubah ya ce, “An kashe mutum hudu. Uku daga cikinsu a Yogboh yayin da sauran kuma aka kashe a Ukohor a cikin wannan lokacin.”
A halin da ake ciki, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, ba ta amsa kiran waya ko sakon tes da aka aika mata a wayar salula kan lamarin ba.
A wani labarin kuma: Tabbas Atiku Zai Sha Kayi A Yankin Arewa Maso Gabas – Inuwa Yahaya
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba shi da damar yin nasara a yankin Arewa maso Gabashin kasarnan.
“Hakika dama mu na da yawa sosai kuma muna da karfi a kudurinmu na yin aiki don samun nasarar babbar jam’iyyar mu,” in ji shi.