Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan tsaro ya ƙaryata wani rahoto dake yawo a kafafen sadarwa na zamani akan naɗa sabon Darkta-Janar na Hukumar Kula binciken sirri da adana su.
Acewar sanarwar wadda aka fitar a ranar juma’a daga Shugaban Kula da Dabarun Sadarwa na ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Zakari Usman.
A cewar Usman “hankalin ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan tsaro ya kai ga wani rahoto da aka fitar a kafar sadarwa ta zamani da aka ce ya fito ga wasu tsaffin Daraktoci da ba’a ambaci sunan su ba na Hukumar Kula da Bayyana sirri akan naɗa sabon Darkta-Janar na Hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen Shuwagabannin APC na Ƙasa: Gwamnoni zasu fitar da ranar da zaɓen a ranar Lahadi
“Kundin tsarin da ya kafa Hukumar ƙarƙashin doka ta shekarar 1986 (Cap 278 LFN), naɗa Darkta-Janar na Hukumar Adana bayanan sirri, Shugaban Ƙasa kaɗai keda damar aikata hakan.
“Ana naɗa Darkta-Janar na Hukumar NIA da bin ƙa’idojin da doka ta tanada.
Mai Magana da Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara ya bayyana cewa Hukumar nada Shugaban ta Ahmed Abubakar wanda shine ke jagorantar ta, tun lokacin da aka naɗa shi.
Ya bayyana cewar Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan tsaro ya gamsu ƙwarai da tattaunawar da ake yi da tsakanin ofishin sa da na Darkta-Janar na Hukumar domin cimma nasarar adana bayanan sirri, wanda ya saɓawa abunda ke cikin ƙagaggen rahoton nan, Abubakar bai faɗi jarabawar ƙarin girma ba, kuma yana cigaba da jajircewa akan ayyukan sa.”
Usman ya bayyana cewar rahoton kenan ya nuna cewa Majalisun Najeriya basu san da naɗa Darkta-Janar kenan ba a shekarar 2018 .
Yayi nuni dacewar Babbar Kotun Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Okon Abang ta kori ƙarar da aka shigar ana ƙalubalantar naɗa Darkta-Janar na Hukumar Adana bayanan sirri.
Mai Magana da Yawun Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara akan tsaro ya yi kira ga Al’umma da dukkanin jami’an tsaro dasu jefar da wannan sanarwa, wadda an ƙirƙire ta ne domin wata manufa.
Comments 1