Mai tsare lafiyar babban Hafsan sojin kasar Ethiopia, ya harbe uban gidan nasa, Janar Seare Mekonnen, tare da wani jami’in soja.
Mutanen biyu sun mutu ne a lokacin da suke kokarin dakile yunkurin juyin mulkin da aka so a yi a yankin Amhara da ke arewacin kasar, in ji FiraiministaAbiy Ahmed.
Baya da mutanen biyu, an kuma kashe gwamnan yankin na Amhara, Ambachew Mekonnen tare da wani mai ba shi shawara.
Gwamnati ta ce yanzu haka komai ya lafa.
Firaiminista Abbiy Ahmed ya shiga gidan talbijin din kasar, inda ya nemi ‘yan kasar da su hada kai su tunkari masu son wargaza kasar.
Amurka dai ta umarci ma’aikatanta da ke birnin Addis Ababa da ka da su fita waje.
Tun da farko Abiy Ahmed ya yi sanarwar yunkurin juyin mulkin ta tashar talabijin din kasar, kuma abin mamaki a can cikin dare, yana sanye da kayan soji na rawar daji.
Ya ce wasu sojin haya sun kai hari kan hafsan sojin, amma kuma bai bayar da cikakken bayani kan halin da janar din yake ciki ba bayan da aka kai masa harin.
Mista Abiy ya kuma kara da cewa an hallaka wasu jami’an gwamnatin yankin na Amhara a lokacin wani zaman taro da abokan aikinsu.
Mazauna unguwar da ke kusa da hedikwatar ‘yan sandan, babban birnin yankin, na Amhara sun ce sun rika jin karar bundugogi ba kakkautawa, a ranar Asabar da yamma a kusa da ginin.