Majalisar Dokokin Jahar Zamfara ta rage yawan kasafin kuɗin da Gwamna Bello Matawalle ya gabatar mata na shekarar 2021, sakamakon ƙarancin kuɗaɗen da ake tattarawa a jahar, wanda rashin tsaro ya haifar a jahar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaru na Majalisar Mustapha Ƙaura, inda yace an rage kuɗi daga Naira biliyan 126.7 zuwa Naira biliyan 117.5.
Ƙaura yace “a dawowar zaman ta, Majalisar tayi dubi akan rahoton kwamitin ta akan Kasafin Kuɗi, inda aka ɗora mashi alhakin duba kasafin kuɗi na shekarar 2021 kamar yadda Sashen Zartaswa ya buƙata satin daya gabata.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Neja ya gaza bayyana gaban majalisa akan lokaci domin gabatar da kasafin 2022
Muƙaddashin Shugaban Kwamitin Shamsudeen Marafa yace bayan dubi akan dukkanin abinda yake bayyane na hujjoji, kwamitin shi baya da wani zaɓi, illa ya rage adadin yawan kasafin kuɗin daga Biliyan 126,775,000.00 zuwa biliyan 117,575,400,000.00.
Yace rashin tsaro ya sanya ba’a samun kuɗaɗen shiga, da kuma abinda cutar Covid-19 ta janyowa jahar dama ƙasa baki ɗaya, ya sanya aka rage yawan kasafin kuɗi.