Majalisar dattawa ta Amurka ta sallami Shugaba Donald Trump a shari’ar da ake ma sa wanda ya kawo karshen yunkurin tsige shi daga mulki da ya raba kan Amurkawa.
Majalisar dattawan wadda ta kasance karkashin ikon ‘yan jam’iyyar Republican ce – wadda kuma ita ce jam’iyar Mista Trump – ta kada kuri’ar wanke shi.
Kan tuhumar farko ta rashin iya aiki, ‘yan majalisar su 52 sun wanke shi daga tuhumar inda wadanda suka nemi a tsige shi su 48 ne.
A karkashin daya tuhumar ta hana majalisa gudanar da aikinta, ‘yan majalisar dattawa 53 ne suka zabi a wanke shugaban, inda 47 kuma suka ce ya aikata laifin.
‘Yan jam’iyyar Democrat ne suka fara tuhumar shugaban a watan Disambar bara bayan da ta bayyana cewa ya yi amfani da mukaminsa na shugaban kasa ya tursasawa shugaban kasar Ukraine ya bata sunan abokin hamayyarsa na siyasa, wato tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden.
A watan Nuwamba mai zuwa Mista Trump zai kasance shugaban Amurka da aka tsige na farko da zai nemi a sake zabensa.
Amma a wani zama mai cike da tarihi da majalisar ta yi Laraba, ta zabi ta kyale shugaban wanda shi ne na 45 cikin jerin shugabannin Amurka da ya ci gaba da mulki.
Da an same shi da laifi, da ya kasance ma sa tilas ya mika mukaminsa ga mataimakinsa Mike Pence.