Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan kasar nan (CJN).
Tabbatar da hakan ya biyo bayan tantance shi da aka yi a zauren majalisar a ranar Larabar nan.
Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa, Ariwoola, yayin da yake amsa tambayoyi kafin a tabbatar da shi, ya ce babban kalubalen da ke gaban bangaren shari’a shi ne rashin isassun kudaden gudanar da ayyukanta.
Ya ce dole ne a ba wa bangaren shari’a kudade, yana mai cewa bai kamata a rika kallon alkalai a matsayin mabarata ba.
KARANTA KUMA: CJN Ya Rantsar Da Sabon Mukaddashin Jojin Abuja
Ya bukaci majalisar dattijai da ta gaggauta amincewa da kasafin kudin bangaren shari’a domin ta samu damar gudanar da ayyukanta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Dangane da zargin cewa wasu alkalai sun rubuta koke a kan tsohon CJN, Ariwoola ya ce babu wani koke game da hakan.
A cewarsa, abin da aka fallasa ga manema labarai shi ne wasikar koke da wasu alkalai 14 suka rubuta a kan batutuwan da suka shafi ayyukan shari’a da bukatar jin dadin jami’an shari’a.
“Mu mutum 14 ne muka rubuta da hannu zuwa ga dan’uwanmu tsohon CJN, yadda abin ya kai ga jaridu, ba mu sani ba, ba mu da wata matsala da lambarmu na daya.
“Babu wani koke game da CJN, ba mu yi zanga-zanga ba, kawai mun sanya korafinmu a takarda ga dan uwanmu,” in ji shi.
Sai dai ya kara da cewa shi ne babban burinsa na bullo da fasahar kere-kere a cikin ayyukan tsarin shari’ar kasar.
Ya kuma ce an samar da injuna don gyara dokoki da tsarin kotuna domin tabbatar da ingantattun ayyukansu.
Ya ce akwai kuma bukatar a nada karin alkalai domin saukaka gudanar da shari’o’i cikin gaggawa, yayin da ya kuma bayar da shawarar cewa a yanke hukuncin karshe kan wasu kararraki a kotunan daukaka kara.
Ya ce wasu daga cikin wadannan batutuwan da suka shafi tsarin mulki ne da ke bukatar gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.
Ya kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa ta taimaka wajen gyara dokoki kan irin wadannan abubuwa.
Akan batutuwan da suka shafi nadin alkalai, ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar ya fito karara kan tsarin nada mukamai.
Ya ce majalisar shari’a ta kasa tana taka muhimmiyar rawa ta hanyar ba da shawarwarin kwararrun jami’an da suka cancanta da za a nada. (NAN)
A wani labarin kuma: Yajin Aikin ASUU: Sojoji Da ’Yan Sanda Sun Dakatar Da Zanga-zangar Dalibai
Jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda sun bazama a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja domin hana shugabannin kungiyoyin dalibai gudanar da zanga-zangar adawa da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yi.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Shugabannin kungiyar Dalibai daga cibiyoyi daban-daban na Kaduna sun yi barazanar tare babbar hanyar a yau a wani mataki na nuna fushinsu kan yajin aikin da ASUU ke yi a kasar.