Shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa Ahmad Lawan ya ce karya ce mararan ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani xewa muna kokarin kawo wani kudiri da zai baiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari damar zarcewa a wa’adi na uku indai har yana son hakan a ran shi.
A wata Sanarwa Mai dauke da sanya hannun Babban Mai tallafa mishi kan harkar yada labarai ya fitar, Ahmad Lawan ya ce shi jo da gigin wasa bai taba wani kalami mai kama da wannan ba tun gabannin gudanar da babban zaben 2019, haka ma bayan zaben babu wata magana mai kama da haka.
Shugaban Majalisar Dattijan ya ce shi ma dan kasa ne kamar kowa don haka ba zai yi Karan tsaye ga kundin tsarin mulki da ya bada damar yin wa’adi biyu kachal kan karagar mulki ba, saboda haka kowa maida wukar sa kube domin babu wannan zancen.
“Abin da Kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya ce shine babu wata kofa ta sauya wa’adin shugaban Kasa a ko wani irin kauli ne, kuma haka yan Najeriya suka yi amanna da shi” Cewar Lawan.
“Sashe na 137 na kundin tsarin mulkin ya bayyana kararra cewa ‘babu wani dan kasa da za’a iya sake zabar shi a muƙamin shugaban Kasa indai har ya taba Kasancewa a wannan muƙamin a wa’adi biyu jere da suka gabata”
“Shugaban Majalisar bai ga wani aibu dangane da dokar b, don babu wani dalili sa zai sa ya yi mata karan tsaye” In Ji Sanarwar.