Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da wani rahoton majalisar dinkin duniya kan matsalolin tsaro a kasar. Cikin wata sanarwa, kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya ce rahoton na wakiliyar majalisar dinkin duniya Agnes Callarmard ta fitar, bai yi adalci ba, wajen fayyace gaskiyar halin da ake ciki kan tsaro a Nijeriya ba.
Martanin na gwamnatin Nijeriya, ya zo ne kusan makonni uku bayan wallafa rahoton. Cikin rahoton, wakiliyar majalisar dinkin duniyar, ta bayyana Nijeriya a matsayin kasar dake fama da rikicin cikin gida da dama, wadanda ke da da kamari, ko da yake rahoton ya yabawa gwamnati kan nasarorin da ta samu kan Boko Haram.
A bangaren tashe-tashen hankula a sauran sassan kasar, rahoton majalisar dinkin duniyar ya bayyana rashin bibiya, talauci, sauyin yanayi da kuma yaduwar muggan makamai a tsakanin jama’a a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke rura wutar matsalolin tsaro da rikice-rikicen da Nijeriya ke fuskanta.
Sauran matsalolin a cewar majalisar dinkin duniya sun hada da, yadda gwamnati ke yin amfani da karfi wajen dankwafe wasu kungiyoyi a Nijeriyar da suka hada da ‘yan shi’a, ‘yan Kungiyar IPOB da aka haramta, da kuma al’ummar Ogoni.
Sai dai gwamnatin Nijeriya ta bayyana bacin rai kan yadda rahoto ya gaza bayyana matakan da take dauka wajen magance matsalolin da ya zayyana.