Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana cewa har yanzu akwai katin zabe 165,631 wadanda ba a karba ba a jihar Kogi ya zuwa ranar 13 ga watan Satumba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da take karin haske dangane da karbar katin zaben a jihar wanda aka fara a ranar 2 ga watan Satumba, a shirye-shiryen zaben 16 ga watan Nuwamba da zai gudana a jihar.
Rahoton INEC din ya tabbatar da cewa cikin makonni biyu an karbi katin zabe 5,269 a Kogi cikin 170,900.
Sakataren watsa labarai ga shugaban INEC din, Rotimi Oyekanmi ya shawarci wadanda suka yi katin zaben da su hanzarta su je su karbi katinsu.