Majalisar dokokin jihar Gombe ta tabbatar da kwamishinoni biyu da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya nada.
Kwamishinonin sun hada da; Sanusi Ahmed Pindiga da Andirya Abishai Moljengo Computer daga kananan hukumomin Akko da Kaltungo an tabbatar da su nan take bayan gwajin da suka yi a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Har Yanzu Ina Son Mijina Dan Boko Haram Inji ‘Yar Makarantar Chibok Da Aka Ceto
Ko da yake, an tantance mutanen biyu a daidaikunsu, sakamakon haka sun yi baka bayan sun gabatar da aikinsu a gaban ‘yan majalisar.
Wakilinmu ya rawaito cewa, an tabbatar da hakan ne biyo bayan murabus din da tsohon kwamishinan yada labarai Julius Ishaya ya yi, wanda ya bar mukaminsa domin ci gaba da harkokinsa na siyasa da kuma dan majalisa kuma tsohon kwamishinan muhalli, Hussaina Goje, wanda ya yi murabus a zazzafar Gwamna Yahaya da Danjuma Goje.
A yayin da suke yaba wa Gwamna Muhammadu Yahaya bisa zabar mutanen da suka dace, ‘yan majalisar daga mazabun kwamishinonin sun bada gudunmawar kuden da suke bayarwa a bangaren gwamnati da masu zaman kansu, tare da bayar da tabbacin cewa kwamishinonin za su bayar da gudunmawa sosai wajen samun nasarar gwamnatin da Yahaya ke jagoranta.
A karshen taron tantancewar, mataimakin kakakin majalisar, Siddi Buba, wanda ya jagoranci atisayen, ya gabatar da tambayar domin tabbatar da su, kuma ‘yan majalisar sun amince da nadin nasu baki daya.
A wata hira da manema labarai, kwamishinonin biyu da aka tabbatar sun bayyana farin cikin su tare da ba da tabbacin cewa a shirye suke su bayar da tasu gudunmawar a duk wani matsayi da za a ba su.
Sannan sun yi alkawarin yin aiki domin samun nasarar gwamnati musamman sake tsayawa takarar gwamna Yahaya.
A wani labarin kuma, PDP Ta Maka Gwamna Abdulrazaq A Kotu Bisa Zarginsa Da Yin Amfani Da Jabun Takardu
An gurfanar da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zarginsa da yin amfani da takardar shaidar kammala karatu ta Yammacin Afirka ta jabu wajen tabbatar da tsayawa takarar Gwamna a zaben 2023 a Jihar.
A karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kansa, an bukaci babbar kotun tarayya da ta haramtawa gwamna da jam’iyyar APC shiga zaben gwamna na shekara mai zuwa.