A wata ziyara da Shugabannin Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi (Kumbotso) bisa Jagorancin Professor Isah Yahaya Bunkure su ka kaiwa Majalisar Dokokin Jihar Kano a yau, Majalisar ta tabbatar da goyon bayanta wajen ganin an daga likkafar Kwalejin Ilimi Mai zurfi ta Sa’adatu Rimi zuwa Jami’a.
Wannan na kunshe a cikin jawabin da Kakakin Majalisar Dokokin, Rt. Hon. Engineer Hamisu Ibrahim Chidari, ya gabatar gaban shugabannin, inda ya ce bisa la’akari da irin dimbin ayyukan da Kwalejin ke yi da kuma inganta ilimi a Jihar Kano, Majalisar za ta goyi bayan kudurin gwamnati na ganin wannan Kwaleji ta zama Jami’a.
Daraktan yada labaran majalisar Uba Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya aikowa da Jaridar Dimokuradiyya a ranar Talata, ya rawaito cewa Rt. Hon. Engineer Hamisu Ibrahim Chidari kara da cewar akan shekarun yin ritaya da kuma shekarun aiki kamar yadda Shugaban Kwalejin ya roka, Majalisar za ta yi nazari akan haka da zaran bangaren Zartarwa sun aiko da bukatar hakan.
Sannan ya godewa jagororin Kwalejin bisa jajircewarsu wajen inganta Ilimi tare da yin kira garesu da su kara zage damtse bisa la’akari da sabbin hanyoyi da dabarun bayar da Ilimi.
A jawabinsa, Shugaban Kwalejin, Professor Isah Yahaya Bunkure ya ce sun kawo wannan ziyara ne domin inganta dangantaka tsakaninsu da Majalisar Dokoki domin kara dankon zumunci.
Sannan ya tabbatarwa da Majalisar cewar makarantar za ta cigaba da rike kambunta wajen bayar da Ilimi Mai nagarta a fadin Kasar nan.