Majalisar kansilolin karamar hukumar Nassarawa ta tsige mataimakin kakakinta kansilar mazabar Kawaji, Mubarak Ali Idris.
Majalisar ta dauki matakinne a zamanta na yau, sakamakon samunsa da laifin saba ka’idojin aiki, da kuma bayyana sirrin karamar hukuma.
Nan take, bayan tsige shine kuma aka maye gurbinsa da kansilan mazabar Kaura Goje, Hamisu Ahmad Agogo tare da bada umarnin mika ofis ga sabon mataimakin shugaban majalisar.
A nasa bangaran sabon mataimakin shugaban majalisar karamar hukumar, Hamisu Ahmad Agogo ya mika godiyarsa bisa zabarsa da akayi.