Ana shirye shiryen fara yajin aiki a Birtaniya, babbar ƙungiyar Malamai ta ƙasar ta sanar da cewa zata shiga yajin aiki saboda matsalar albashi a Ingila da Wales. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Haɗadiyar ƙungiyar harakokin ilimin ƙasar (NEU) tace mambobin ta sun amince da su gudanar da tattaki a matsayin hanyar kiraye kiraye ga hukumomi akan tashin farashin kayyaki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Najeriya Miliyan 25 Na Fuskantar Barazanar Yunwa — UNICEF
Sanarwa na zuwane ne a dai dai lokacin da Ma’aikatan gwamamnati suka gudanar da wasu tattaki domin nuna damuwarsu aka tashin farashin kayyaki dake cigaba da ƙaruwa.
A wani taro da ya halartar ta kafar Intanet tare da mambobin ƙungiyar sakatare Ƙungiyar malamaman ta ƙasa Birtaniya Kevin Courteney yace yayi ammana gwamamnatin tana da masaniya akan buƙatar da ke akwai na yin gyara a bangaren albashin malamai.
Bayanai sun nuna cewa , Shugabanin kungiyar za su gana da da ministan ilimin ƙasar a ranar Laraba.
Sai dai ƙungiyar ta ayyana yajin aiki a faɗin ƙasar da zai fara a ranar 1 ga watan Fabrairu shekarar nan, tare da ci-gaba da yajin aikin a sauran yankunan na tsawon kwanaki 6 a cikin watan na Fabrairu zuwa Maris.
Lamarin dai zai shafi kowace makaranta na tsawon kwanaki huɗu ne.
Sai dai lamarin zai shafi tare da sanya damuwa ga iyayen yara, musamman waɗanda ke ganin ilimin ‘ya yansu ya samu koma baya sanadiyar ɓarkewar cutar Korona.
Mambobin cibiyoyin harakokin Ilimi a Scotland zasu fara dakatar da ayyukan koyarwa a ranar Laraba na tsawon kwanaki 16 har zuwa ranar 6 ga Fabrairu.
Tun a baya an sha gudanar da yajin aiki musamman a watan Disamba da farkon wannan watan.
A wannan makon ma’aikatan jinya a Ingila, Wales da arewacin Ireland su ma suna ƙoƙarin cigaba da da yajin aikin a ranakun Laraba da Alhamis.
A wannan makon ne ake sa ran Ma’aikatan jinya da ma’aikatan bayar da agajin gaggawa ke shirin yanke hukunci kan kara ci gaba da gudanar da yajin aikin, tare da ƙarawa Hukumar Lafiya ta Kasar matsin lamba akan abubuwan da ya kamata ta aiwatar a dai dai lokacin da take cigaba da fafutukar ganin ta murmurewa daga jinkirin da cutar Korona ta haifar.
A wani labarin kuma, Ba Zamu Taba Fita Daga Kakanikayi Ba Matukar Muna Siyasa Kan Abu 1 — Buhari
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, Injiniya Yusuf Buhari ya bayyana cewa siyasar kudi ba za ta iya fitar da ‘yan Najeriya daga cikin kalubalen da suke fuskanta ba.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ibadan, da yammacin ranar Litinin