Gwamnatin jihar Adamawa ta ce ba ta shirin kakaba haraji da yawa kan kayan abinci da dabbobi, ba kamar yadda ake yi a wasu jihohin ba.
Alhaji Hamman-Adama Njabari, Shugaban Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida ta Jihar ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai a Yola ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Zamu Taba Fita Daga Kakanikayi Ba Matukar Muna Siyasa Kan Abu 1 — Buhari
A cewarsa, hukumar ta na karbar kudaden shiga ne a kan bayanan motoci, bisa tsarin kasa, kuma ta sabawa duk wata tuhuma da ta saba wa doka.
“Muna rokon direbobi su biya lasisin tuki da sauran bayanan da suka dace,” in ji Njabari.
Ya ce adadin Naira 3,000 shi ne kudin da ake karba kan kowane shanu da ake fitar da su daga jihar, sabanin Naira 5,000 na farko da aka gabatar a baya.
A cewar shugaban hukumar har ila yau, hukumar tana karbar Naira 150 kan kowace buhun hatsi da sauran kayan abinci, sabanin Naira 300 na farko.
Ya bayyana cewa a kwanakin baya ne Gwamna Ahmadu Fintiri ya sake duba kudurin bayan an yi nazari sosai.
“Gwamnan ya rage adadin a matsayin na wucin gadi na rage harajin dabbobi da hatsi, don bayar da tallafi ga masu biyan haraji.
“Muna karbar haraji kan fatu, da kuma masu harajin kaya da ake jigilar su, amma ba ma direbobi ko motocin da ke kai irin wadannan kaya ba.
Ya ce ya kamata masu biyan haraji su fahimci cewa ana karbar haraji ne domin tabbatar da samar da muhimman ababen more rayuwa da sauran ayyukan zamantakewa.
Wani direban babbar mota a Yola, Adamu Mohammed, ya tabbatar wa NAN cewa an bukaci direbobin ne su biya kudin bayanan loda kayan motar su.
A wani labarin kuma, Yan Najeriya Miliyan 25 Na Fuskantar Barazanar Yunwa — UNICEF
Kusan ‘yan Najeriya miliyan 25 na fuskantar barazanar yunwa tsakanin watan Yuni da Agustan shwkarar 2023, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, a cewar wani kididdigar bincike da Cadre Harmonisé, gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar kan abinci mai gina jiki sau biyu a shekara.
Punch ta ruwaito cewa, Wannan dai wani kari ne da aka yi kiyasin cewa mutane miliyan 17 ne ke fuskantar barazanar karancin abinci a halin yanzu.