Manyan kuskure biyu da mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker ya yi sun taimaka wa Manchester City zura ƙwallo har huɗu a ragar zakarun na gasar Firimiyar Ingila a wasan mako na 23.
Kazalika, ƙungiiyar ta Guardiola ta bayar da tazarar maki biyar a saman teburin gasar.
Gündogan ne ya fara zira ƙwallo a minti na 49 bayan ya zubar da finareti kafin a tafi hutun rabin lokaci sakamakon ƙetar da Fabinho ya yi wa Sterling.
Mohamed Salah ya farke wa Liverpool a minti na 63 daga bugun finareti kafin daga bisani Sterling da Foden su ƙara ta uku da ta huɗu.
Yanzu haka akwai tazarar maki 10 tsakanin City a saman teburi da kuma Liverpool a mataki na huɗu bayan wasan da aka buga a Anfield.