Akwai yiwuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa dake ƙasar Birtaniya ta saki dan wasan tsakiyarta Jack Greelish bayan da Manchester City ta jajiɓe madaran kuɗi don sayen shi.
Rahotanni sun ruwaito cewa City ta buɗe lalitar ta ne inda ta kirga tsabar kudi har yuro miliyan casa’in don jajuɓo dan wasan, farashin da ake gani Villa ba ta isa mayarwa ba.
A wani labarin kuma, yayin da har yanzu take kasa tana dabo tsakanin Manchester United da dan wasan tsakiyarta Paul Pogba, yanzu haka kungiyar Paris St German ta kasar Faransa ta ce ware kuɗi har yuro miliyan miliyan 43 inda ta ce idan United din ba za ta iya ba to ita kam tana bukata.
A bangaren abokiyar hamayyar United din wato Arsenal, ita ma dai haka zance yanke inda kwantiragin dan wasan gabanta Alexandre Lacaztte ke gabda karewa, akwai yiwuwar ta yi asara a kanshi ganin cewa ba lallai ba ne ya ci gaba da zama a Ƙungiyar, kuma Ƙungiyoyi da suka taya shi sun taya ne kan yuro miliyan sha biyar alhalin kuma a hamsin da biyu ta saye shi a 2017.
A hannu guda kuma har yanzu a Arsenal din, har yanzu dai ta ce ba ta fidda rai kan dan wasan Leicester City James Madison ba, inda ake ganin za su iya bani gishiri in baka manda da wani dan wasa don dauko shi ko ta halin kaka.